A tsakanin watanni shida kacal an samu nasarar lalata haramtattun matatun mai guda dubu 8 a Najeriya
2024-09-30 10:45:53 CMG Hausa
Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya tabbatar da samun nasarar lalata haramtattun matatun mai har dubu 8, tare kuma da cire layukan da barayi ke amfani da su wajen zukar mai daga bututun mai mallakin kamfanin har dubu 5,800.
Babban jami’in harkokin sadarwa na kamfanin Mr Olufemi Soneye ne ya tabbatar da hakan ranar Asabar 28 ga wata a birnin Abuja yayin wani taro da kamfanin ya shiryawa ’yan jaridu dake aiki a zauran majalissar dokokin kasar.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
A kan batun kara yawan adadin danyen mai da Najeriya ke hakowa a duk rana kuwa, Mr. Olufemi ya tabbatar da cewa, za a iya cimma nasarar hako ganga miliyan uku a duk rana muddin dai aka samu fahimta ta aiki tare a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki, wadanda suka kama daga hukumomin tsaro, gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kamfanonin mai da kuma al’umomin da suke zaune a wuraren da ake hako man.
Ya tabbatar da cewa, suna sa ran samun fahimta da hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki wajen yaki da barayin mai da kuma ’yan ta’adda masu lalata bututun mai, wanda hakan zai bayar da damar ci gaba na adadin man da ake hakowa yanzu haka daga ganga miliyan 2.5 zuwa miliyan 3. (Garba Abdullahi Bagwai)