logo

HAUSA

Babbar hukumar sadarwa CSC ta Burkina Faso ta janye tashoshin RFI guda 5

2024-09-29 15:30:34 CMG Hausa

A kasar Burkina Faso, a ranakun 27 da 28 ga watan Satumban shekarar 2024 ne babbar hukumar sadarwa ta CSC ta yi wani zaman taron a cibiyarta dake birnin Ouagadougou domin nazarin halin kafofin watsa labaru na kasashen waje dake watsa labaru ta dogon zango ko ta gajeren zango.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Daga bisani a karshen wannan zaman taro, mambobin babban hukumar sadarwa ta CSC ta Burkina Faso, bisa babban rinjaye ne, suka yanke shawarar janye tashoshin gidan rediyon kasar Faransa RFI biyar dake watsa shirye-shirye a kasar.

Hakan ya biyo bayan wani zaman taron na hukumar CSC.

Shi dai wannan mataki ya shafi biranen da suka hada da Ouagadougou, Bobo-Dioulasso, Koudougou, Banfora da kuma Ouahigouya da suka kasancewa manyan birane na kasar Burkina Faso da suke fi yawan al’umma.

Shugaban babban hukumar sadarwa ta CSC, Louis Modeste Ouedraogo ya bayyana cewa, wannan na bayyana manufofin gwamnatin soja ta Burkina Faso na kiyaye zaman lafiya da zaman jituwa tsakanin al’umomi da kuma yin alla-wadai da yadda gidan rediyo RFI ya yi kokarin kawo baraka a cikin kasar ta hanyar shirye-shirye da rahotanni da ke bayyana karara goyon baya ga ayyukan ta’addanci.

Ku rike cewa, gwamnatin kasar Burkina Faso ta dakatar da wannan kafar Faransa tun cikin watan Disamban shekarar 2022, bayan zargin wannan tasha da watsa shirye-shiryen goyon bayan ta’addanci da kuma neman gurbata zaman jituwa tsakanin al’umomin wannan kasa dake yammacin Afrika, da kuma take cikin gamayyar kasashe uku na yankin Sahel AES da suka da Nijar, Mali da Burkina Faso. (Mamane Ada)