logo

HAUSA

Hukumomin kasar Benin sun tarbi wani jirgin ruwan soja na kasar Rasha

2024-09-29 15:41:29 CMG Hausa

A kasar Benin, shugaba Patrice Talon ya amince da zuwan wani jirgin ruwan soja na kasar Rasha da ya yada zango a tashar ruwan Cotonou, jirgin ruwan mai suna Smolny ya samu tarbo daga sojojin ruwan kasar Benin a ranar jiya Asabar 28 ga watan Satumban shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A cewar masu fashin baki, zuwan wannan jirgin ruwan soja Smolny na kasar Rasha, a tashar ruwan birnin Cotonou na shaida wata alama ta kyakkyawar huldar dangantaka dake tsakanin kasashen Benin da Rasha.

Smolny ya samu babban tarbo daga manyan sojojin ruwan kasar Benin, a karkashin jagorancin kaftin Dossa Hounkpatin, manjo-janar sojojin ruwan Benin.

Bayan bikin tarbon wannan jirgin ruwa, wani rangadi an gani da ido a cikin jirgin ya gudana tare da jagorancin janar Oleg Gourinov, shugaban wannan ziyarar sada zumunta, da kuma kaftin, Dmitri Parakhine, kwamandan din jirgin ruwan Rasha na Smolny.

Kaftin Dossa Hounkpatin da jakadan kasar Rasha dake Benin Igor Evdokimov sun ziyarci dukkan bangarorin wannan jirgin ruwan soja na Rasha.

Kafin zuwan jirgin ruwan soja na Rasha, an yi wata ganawa a birnin Cotonou tsakanin jakadan kasar Rasha da kuma kaftin Emil Siemba Sama, mataimakin manjo-janar na sojojin ruwan Benin. Inda bangarorin biyu suka maida hankali kan batun dangantakar soja dake tsakanin kasashen biyu. (Mamane Ada)