Kasar Sin ta nuna damuwa kan rikicin Isra’ila da Lebanon
2024-09-29 16:05:38 Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Lahadi cewa, kasar Sin na bin diddigin kisan shugaban kungiyar Hizbullah, Hassan Nasrallah, wanda ya mutu a wani harin sama da aka kai a birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon a ranar 27 ga watan Satumba.
Sanarwar ta ce, kasar Sin na adawa da keta ’yancin kai da tsaron kasar Lebanon, tana adawa da kuma yin tir da duk wani mataki kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma nuna adawa da duk wani mataki da ke rura wutar kiyayya da ta da zaune tsaye a yankin.
Kana kasar Sin ta bukaci bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su gaggauta daukar matakai don kwantar da hankula, da kuma hana tsananta rikicin, ko ma kara tabarbarewarsa. (Yahaya)