logo

HAUSA

Rundunar PLA ta gudanar da atisaye a teku da samaniya kusa da tsibirin Huangyan

2024-09-28 20:07:17 CMG Hausa

A yau Asabar rundunar sojojin ‘yantar da al’ummar kasar Sin PLA ta yankin kudanci, ta gudanar da atisayen sojin ruwa da na sama, a teku da samaniya, kusa da tsibirin Huangyan na Sin.

Atisayen wanda aka saba gudanarwa a kai a kai a wannan karo ya mayar da hankali ga ayyukan sanya ido kan abokan gaba, da hanzarta bayar da gargadi, da kuma sintiri a teku da samaniya. (Saminu Alhassan)