logo

HAUSA

Shugaba Xi zai halarci bikin ajiye furanni don girmama ‘yan mazan jiya

2024-09-28 20:24:38 CMG Hausa

Ranar Litinin 30 ga watan nan na Satumba, rana ce ta tunawa da jarumai ‘yan mazan jiya ta kasar Sin. Kuma da safiyar ranar shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran shugabannin kasar, da ma al’ummun kasar daga dukkanin fannoni na rayuwa, za su halarci bikin ajiye furanni a hasumiyar tunawa da gwarazan ‘yan mazan jiya na kasar Sin, dake babban dandalin Tiananmen na tsakiyar birnin Beijing.  (Saminu Alhassan)