logo

HAUSA

Xi Jinping: Inganta gina dunkulewar kabilun kasar Sin baki daya

2024-09-27 16:47:44 CMG Hausa

An gudanar da taron yabon hadin kai da ci gaban kabilu na kasar Sin a nan birnin Beijing da safiyar yau Jumma’a. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kuma ya gabatar da muhimmin jawabi.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, hanyar warware batutuwan da suka shafi kabilu irin na kasar Sin, ta mayar da hankali ne kan muhimmiyar moriyar al'ummar kasar Sin baki daya, tana iyakacin kokarin hadin kan kabilu daban daban, kana tana mai da hankali kan daidaiton dukkan kabilu, kuma tana adawa da zaluntar kabilu da nuna bambancin kabilu. An riga an shaida cewa, wannan tafarki ya yi daidai. Don inganta zamanantarwa irin na kasar Sin da kuma samun ci gaba tare, ba za a bar wata kabila a baya ba. Dole ne a dage wajen tabbatar da kyautata rayuwar jama'a yayin ci gaba, tare da ci gaba da biyan muradun al'ummomin kowane kabilu na samun ingantacciyar rayuwa.

Ya kuma jaddada cewa, dole ne mu ci gaba da sa kaimi ga hadin kai da ci gaban kabilu, da sa kaimi ga gina dunkulewar al'ummar kasar Sin baki daya, da yin kokari ba tare da kakkautawa ba, wajen sa kaimi ga gina kasa mai karfi da farfado da kasa bisa zamanantarwa irin na kasar Sin. (Safiyah Ma)