logo

HAUSA

An yi liyafar murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin a Nijar

2024-09-27 11:52:44 CMG Hausa

 

Jakadan Sin dake Nijar Jiang Feng ya kaddamar da liyafar murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar Sin a ofishin jakadancin Sin dake kasar a daren ran 25 ga wata.

Jiang ya ce, huldar kasashen biyu ya samu ci gaba mai armashi a wannan shekara da muke ciki. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Abdourahamane Tiani sun kai ga matsaya daya wajen daga huldarsu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare, don jagorantar hanyar bunkasuwar huldarsu, kuma fraministan kasar Nijar Lamine Zeine ya halarci taron kolin dandanlin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka da aka gudana a Beijing bana. Matakin ya bayyana cewa, mabambantan jami’an kasashen biyu na kara mu’amala da cudanya da zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban, ciki har da manyan ababen more rayuwa da sadarwa da makamashi da jinya da sauransu, lamarin ya amfanawa al’umommin kasashen biyu sosai.

Mambobin kwamitin ceton kasar Nijar da mambobin gwamnati da dai sauran muhimman jami’ai na kasar sun bayyana cewa, ana jinjinawa ingantaccen ci gaban da Sin ta samu, wanda ya zama abin koyi na zamanintar da al’umma da farfado da raya kasashe masu tasowa ciki har da Nijar. Shugabannin kasahen biyu kuma sun kai ga matsaya daya na daga matsayin huldar kasashen biyu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare, matakin ya samar da makoma mai haske ga kasashen biyu, da ma kara kwarin gwiwa kan hadin kan kasashen biyu. (Amina Xu)