logo

HAUSA

Babban taron samar da kayayyaki na 2024 ya sa kaimi ga kulla ayyukan hadin gwiwa 718

2024-09-27 14:58:43 CMG Hausa

 

A yayin taron manema labarai da aka shirya a jiya Alhamis, an bayyana cewa, an sa kaimi ga cimma matsaya daya wajen gudanar da ayyuka har 718 cikin hadin gwiwa, a yayin babban taron samar da kayayyaki na shekarar 2024. Yawan kudin da za a zuba a wadannan ayyukan zai kai fiye da dala biliyan 52.6.

A yayin taron na wannan karo, an kebe yankunan baje koli 9 da fadinsu ya kai muraba’in mita dubu 20, wanda ya jawo kamfanoni mahalarta 451, kana yawan samfurorin kayayyakin da aka baje kolin su ya kai 2605, daga cikinsu kayayyakin da aka baje su a karon farko sun kai 236.

Taron ya gabatar da ci gaban da Sin take samu a cikin shekaru 75 da suka gabata, tun kafuwar jamhuriyar al’ummar Sin, a fannin kyautata daga matsayin tsoffin masana’antu, da nazari, da habaka sabbin sana’o’i, da tsare-tsaren da za a dauka a nan gaba, inda aka baje kolin sabbin kayayyaki, da kimiyya da fasahohi na masana’antun samar da kayayyaki na duniya.

Wannan taro ya zama irinsa dake karbar mahalarta daga kasashe da yankuna, da baki mahalarta mafiya yawa a duniya, wanda ke shafar kasashe da yankuna 41. (Amina Xu)