logo

HAUSA

Xi zai raba lambobin yabo na kasa gabanin bikin ranar kafuwar kasar Sin

2024-09-27 19:13:58 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai raba lambobin yabo, da na karramawa na kasa, gabanin bikin cikar janhuriyar kasar Sin shekaru 75 da kafuwa. Za a gudanar da bikin mika lambobin yabon ne da karfe 10 na safiyar ranar Lahadi mai zuwa, a babban zauren taruwar jama’a dake tsakiyar birnin Beijing.

Kaza lika, yayin taron gabatar da lambobin, shugaba Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar zai gabatar da muhimmin jawabi.  (Saminu Alhassan)