“Labarina Game Da Kasar Sin”
2024-09-26 11:08:38 CMG Hausa
Assalamu Alaikum abokai! A wannan lokaci da muke murnar cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyyar Jama’ar kasar Sin, muna fatan za ku shiga wannan shirin da muka shirya mai taken “Labarina Game Da Kasar Sin”.
Za ku iya shiga shirin ta hanyoyi daban daban, kaman rubuta labaranku kai tsaye a shafinmu na FACEBOOK, ko aika mana hotuna da bayanan da abin ya shafa ta e-mail na adireshin hausa@cri.com.cn. Kana, idan kuna son yin bidiyo, muna maraba da ku wallafa shi a shafinku, bisa wannan take na “Labarina Game Da Kasar Sin”, da kuma @ shafinmu wato CGTN Hausa, domin mu zabi wasu daga cikinsu, sa’an nan, mu wallafa a karin shafukanmu da ma dandali daban daban, da kuma bayyana labaranku cikin shirye-shiryenmu masu farin jini.
Daga fitar da biliyoyin mutane daga kangin talauci, zuwa fitar da motoci masu amfani da sabbin makamashi, da batir irin na Lithium, da kayan amfani da hasken rana da kasuwannin kasashen duniya, har da wani wasan bidiyo game na kasar Sin mai suna “Black Myth: Wukong” sun samu karbuwa a wasu kasashen duniya, wanda ya sa jama’ar kasashen suka kara fahimtar kyawawan al’adun gargajiya na Sin.
Cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, kasar Sin ta sami gagarumin sauyi. Mai yiyuwa ka/kin taba ziyartar kasar Sin, ko yin karatu ko kuma yawon shakatawa da sauransu. Mai yiyuwa ba ka/ki taba ziyartar kasar Sin ba, amma ka/kin taba amfani da kayayyaki kirar Sin, kuma kana/kina fatan ziyartar kasar Sin domin kara fahimtar al’adun gargajiya da tarihin kasar Sin, da bunkasuwar fasahohin zamani a sassan kasar. Muna son sauraron fatanku da kuma labaranku game da kasar Sin, da fatan za ku bayyana mana labaranku da kasar Sin. Mun gode!