logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da dawowar kasar Nijar cikin aikin tsaron hadin gwiwa

2024-09-26 08:59:39 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar jiya Laraba 25 ga wata cewa, jamhuriyyar Nijar ta amince da dawowar dakarunta cikin aikin tsaron hadin gwiwa a yankin Sahel.

Ministan tsaro Alhaji Badaru Muhammad ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labaru a birnin Abuja a jerin hidindimun da ake yi kan bikin ranar tsoffin sojojin kasar na shekara ta 2025 wanda za a gudanar cikin watan Janairu mai zuwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ita dai wannan hadakar jami’in tsaron hadin gwiwa, kasashen dake yankin tafkin Chadi ne suka samar da ita da nufin yaki da ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da ake aikatawa a tsakanin kasa da kasa, to amma dai tun bayan ficewar kasar Nijar daga kungiyar Ecowas a watan Janairun 2024 ta dakatar da shigar sojojinta cikin shirin aikin tsaro na hadin gwiwa.

Kamar dai yadda ministan ya yi magana ta bakin babban sakataren ma’aikatar tsaro ta kasa Dr Abubakar Kana, ya bayyana dawowar kasar ta Nijar cewa,  yana daga cikin kokarin babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa bayan ziyarar da ya kai Jamhuriyar ta Nijar a watan da ya gabata.

Alhaji Muhammad Badaru haka kuma ya ce, hakika sake shigowar dakarun kasar ta Nijar cikin aikin tsaron hadin gwiwar zai kara taimakawa sosai wajen inganta tsaro a kan iyakokin dake tsakanin Najeriya da kasar, sannan kuma zai kara azama sosai ga dakarun tsaron hadin gwiwar.

A kan kokarin dakarun tsaron Najeriya kuwa a cikin gida, ministan ya ce, a halin yanzu an samu raguwar matsalolin tsaro da kusan kaso 65 a dukkan sassan kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)