Kasar Sin na cikin jerin kasashe 3 dake kan gaba a fannin cinikayya ta dijital a duniya
2024-09-26 15:14:14 CMG Hausa
An fitar da rahoton ci gaban harkokin cinikayya ta dijital na duniya na 2024, wanda shi ne rahoto karo na 3 na baje kolin cinikayya ta dijital na duniya.
Cikin rahoton wanda mashirya baje kolin da cibiyar raya cinikayya ta duniya suka tsara, an yi kiyasin tsakanin shekarar 2021 da 2023, yawan cinikayya ta dijital na duniya ya karu daga dala triliyan 6.02 zuwa dala triliyan 7.13, inda matsakaicin karuwarsa a shekara 1 ya kai kaso 8.8 bisa dari. Daga cikin manyan kasashe 10 masu karfin tattalin arzikin a duniya, Tarayyar Turai da Amurka da Sin, sun kasance kan gaba a fannin yawan irin wannan cinikayya, kuma suna samun ci gaba ba tare da tangarda ba. (Fa’iza Mustapha)