An fitar da rahoto game da wanzar da ci gaban hada hadar sufuri ta Sin
2024-09-25 19:33:05 CMG Hausa
A yau Laraba ne aka gudanar da dandalin kasa da kasa na wanzar da hada hadar sufuri na shekarar 2024, karkashin ma’aikatar sufuri ta Sin. Yayin taron na yini 2, wanda ya gudana a birnin Beijing bisa taken "Sufuri mai dorewa: Hidimar aikewa da hajoji mai hade duniya", an fitar da rahoton wanzar da ci gaban hada hadar sufuri na kasar Sin na shekarar 2023.
Rahoton da aka fitar ya nuna tsarin hade sassan kasa da kasa ta fuskar sufuri, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya na gudana bisa daidaito.
A fannin sufurin kasa tsakanin sassan kasa da kasa kuwa, Sin ta sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa da daidaikun kasashe, da kuma na kasa da kasa har 22, kana ta bude hada hadar sufuri ta kasa da kasa da tashoshi 68.
A shekarar 2023, jimillar hajojin da aka yi jigilar shige da ficen su a kasar Sin ta hanyoyin mota sun kai tan miliyan 92.5284. A lokaci guda kuma, Sin ta gaggauta gina hanyar siliki ta sama, tare da sanya hannu kan takardun yarjeniyoyin sufurin sama tare da kasashe 105. (Saminu Alhassan)