logo

HAUSA

An fitar da rahoton farko game da ci gaban cinikayyar dijital na Sin

2024-09-25 19:06:47 CMG Hausa

An fitar da rahoton farko game da ci gaban bunkasar cinikayyar dijital na Sin yau Laraba a birnin Hangzhou na kasar Sin, yayin taron kasa da kasa karo na 3, na baje kolin hada hadar kasuwancin dijital, rahoton da ya fayyace yanayin da ake ciki, da manufofi da ka’idoji, da halin bunkasar cinikayyar dijital na kasar Sin.

Yanzu haka dai kasar Sin ce kan gaba cikin shekaru 11 a jere, a fannin hada hadar cinikayyar hajojin sayayya ta yanar gizo. A watanni 6 na farkon shekarar bana, hada hadar cinikayya ta yanar gizo tsakanin sassan kasa da kasa na kasar Sin ya kai kaso 5.7 bisa dari, yayin da yawan jarin kai tsaye na waje a fannin raya tattalin arzikin dijital na Sin ya karu da kaso 30 bisa dari. (Saminu Alhassan)