logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci tattaunawa tsakanin ministocin wajen Sin da kasashe mambobin CELAC hudu

2024-09-25 20:38:41 CMG Hausa

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci tattaunawa zagaye na takwas, tsakanin ministocin harkokin waje na Sin da na kasashe mambobin kungiyar kasashen Latin Amurka da Karebiya ko CELAC guda hudu, taron da ya gudana a hedikwatar MDD dake New York a jiya Talata. Wakilai daga dukkan kasashe mambobin CELAC su ma sun halarci taron. 

Kuma a jawabinsa, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da tsayawa tsayin daka kan madaidaicin ra’ayi na adalci, da cimma moriya tare, da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Latin Amurka da Karebiya, da aiwatar da manyan ajandoji guda uku na duniya, da hada aikin gina shawarar ziri daya da hanya daya, tare da tsare-tsaren ci gaban kasashen, ta yadda za a kawo alherai ga sassan biyu. (Safiyah Ma)