logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen Habasha

2024-09-24 20:45:59 CMG Hausa

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Habasha Taye Atske-Selasie a birnin New York na kasar Amurka a jiya Litinin.

Yayin zantawar, Wang Yi ya ce kasar Sin na son yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, ciki har da Habasha, don gaggauta aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin Beijing, na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da yin hadin kai wajen samun bunkasuwa da farfadowa.

Taye ya ce, Habasha ta yi matukar amincewa da kasar Sin, don gane da harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi, kuma tana son karfafa hadin gwiwa wajen nuna adawa da ra'ayin bangaranci da nuna fin karfi, ta yadda za su kiyaye adalci tsakanin kasa da kasa. (Safiyah Ma)