logo

HAUSA

Sin ta kadu da rasuwar mutane da dama sakamakon hare-haren Isra'ila kan wasu sassan Lebanon

2024-09-24 19:54:17 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum a yau Talata. Yayin taron, wani dan jarida ya tambaye shi game ikiranin da ma'aikatar kiwon lafiyar jama'a ta Lebanon ta yi cewa a jiya Litinin, hare-haren da Isra'ila ta kai wasu sassan Lebanon daga sama sun haddasa mutuwar mutane 492, da jikkatar mutane 1645, wanda hakan ya sanya ranar zama mafi samun asarar rayuka a rikicin Lebanon da Isra'ila cikin shekara guda. 

Game da hakan Lin Jian ya ce bangaren Sin yana mai da hankali sosai kan halin tashin hankali da ake ciki a yanzu tsakanin Lebanon da Isra'ila, kuma asarar rayukan da matakan soji suka haifar ya bakanta ran bangaren Sin. Kaza lika, gwamnatin Sin tana adawa da ayyukan keta ikon mulkin kasa da tsaron Lebanon, kuma tana adawa, da kuma yin tir da duk wasu ayyuka da ke cutar da fararen hula.

Game da yunkurin Amurka na dakile kamfanonin Sin daga bayar da hidimomin shimfida wayoyin sadarwa na cikin teku na duniya, Lin Jian ya ce, Amurka tana sanya siyasa, da batun tsaro cikin harkokin da suka shafi fannin, wanda hakan ya zama babbar barazana ga ka'idodin kasuwanci na duniya. Kuma tabbas gwamnatin Sin na matukar adawa da hakan. (Safiyah Ma)