Sin za ta bincike kamfanin Amurka bisa zargin nuna wariya a fannin cinikayya
2024-09-24 18:59:23 CMG Hausa
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce za ta binciki kamfanin PVH na Amurka, karkashin tanajin ka’idojin dakile kamfanoni da ba za a iya dogaro da su ba, sakamakon zarginsa da ake yi da karya ka’idojin cinikayya, da sabawa wasu tanade-tanaden kasuwanci masu nasaba da hajojin dake fitowa daga jihar Xinjiang ta kasar Sin.
An dai zargi kamfanin na Amurka da kauracewa sayen albarkatun auduga daga jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai ba tare da gabatar da sahihin dalili ba, wanda hakan ya keta hakki da moriyar kamfanonin Sin masu nasaba da batun, kana hakan ya jefa ‘yancin mulkin kai na Sin cikin hadari, tare da gurgunta tsaro, da ci gaban moriyar kasar, kamar dai yadda ma’aikatar cinikayyar ta Sin ta bayyana. (Saminu Alhassan)