logo

HAUSA

EU ta tallafawa Najeriya da wasu kasashe 5 da annobar ambaliyar ruwa ta sha da tsabar kudi har sama da euro miliyan 5

2024-09-24 09:46:11 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Turai ta samar da tallafin kudade har euro miliyan 5 da dubu dari 4 ga Najeriya da wasu kasashe 5 dake yankin Sahel wanda suka gamu da mummunar annobar ambaliyar ruwa.

Kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Litinin 23 ga wata a birnin Abuja, ta zayyano kasashen Chadi, Jamhuriyar Niger, Kamaru, Mali da kuma Burkina Fasso a matsayin wadanda za su amfana da wannan tallafin kudi.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////

 

Sanarwar wadda take dauke da sa hannun kwamashinan lura da kare afkuwar bala’o’i na kungiyar EU Mr. Janez Lenarcic, ta nuna cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa mutane sama da miliyan 4 da dubu dari 4 dake wadanan kasashen wanda annobar ta shafa, ta hanyar samar musu da muhalli, kayan abinci, ruwan sha mai tsabta da sauran kayan bukatun rayuwa wanda suka rasa sakamakon ambaliyar ruwa.

Kamar dai yadda yake kunshe cikin sanarwar, kasar Chadi za ta samu euro miliyan 1 daga cikin wannan adadin kudi, yayin da Jamhuriyar Nijar za ta samu euro miliyan 1 da dubu 350, Najeriya kuma za ta samu euro miliyan 1 da dubu dari 1, kasar Mali kuma za ta samu euro miliyan 1, sai Kamaru euro dubu 650 yayin da kasar Burkina Faso za ta rabauta da euro dubu dari 3.

Wannan dai kamar yadda kungiyar ta EU ta sanar kari ne a kan euro miliyan 232 na taimakon jin kai da kungiyar ta baiwa wadannan kasashe a cikin wannan shekarar da muke ciki. (Garba Abdullahi Bagwai)