Shugaban Najeriya ya ba da umarnin dakile safarar motocin sata
2024-09-24 13:46:31 CMG Hausa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su murkushe mutane dake da hannu a safarar motocin sata, matakin dake da nufin kara karfafa da kare mutuncin tattalin arziki kasar daga ayyukan miyagu.
A cikin wata sanarwar da aka fitar a yammacin Lahadi, Tinubu ya ce Najeriya za ta ci gaba da hada kai da kawayenta na kasa da kasa wajen ganin an hana masu aikata laifuka ta yanar gizo da gungun barayin motoci tsakanin kasa da kasa cin gajiyar ayyukansu.
Ya kara da cewa, “Najeriya ba dandalin motocin sata da matattarar dukiyar haram daga kasashen ketare ba ce.” Yana mai tabbatar da cewa, gwamnatinsa a shirye take ta magance matsalar satar kudade, laifukan yanar gizo, da sauran laifukan kudi. (Mohammed Yahaya)