Xi Jinping ya taya Anura Kumara Dissanayake murnar kama mukamin shugabancin kasar Sir Lanka
2024-09-23 15:14:40 CGTN Hausa
Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga Anura Kumara Dissanayake don taya shi murnar kama aiki a matsayin shugaban kasar Sir Lanka.
A sakon nasa, Xi ya ce, Sin da Sir Lanka makwabta ne masu dadaden zumunci. A cikin shekaru 76 da suka gabata tun kafuwar huldar diplomasiyya tsakaninsu, kasashen biyu na samun fahimtar juna da goyawa juna baya, matakin da ya zama abin koyi na huldar kasashe masu mabambantan girma da hadin gwiwa tare da amfanawa juna. Shugaba Xi ya ce, Sin na daukar raya huldar kasashen biyu da muhimmanci, yana kuma mai fatan hadin gwiwa da takwaransa na Sir Lanka, don kara raya zumuncinsu da zurfafa amincewa da juna a bangaren siyasa da ma ingiza samun ingantaccen ci gaba cikin hadin gwiwa karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma sa kaimi ga taimakawa juna da raya huldar abota ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare zamani bayan zamani, ta yadda za a kara amfanawa al’umommin kasashen biyu. (Amina Xu)