Rahoto : Masana'antun dab’i na dijital ta kasar Sin ta habaka cikin sauri a 2023
2024-09-23 10:39:08 CMG Hausa
Rahoton shekara-shekara na cibiyar nazarin aikin jarida da dab’i ta kasar Sin ko CAPP ya nuna cewa, darajar masana’antun dab’i na dijital ta kasar Sin ta kai yuan triliyan 1.618 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 228.89 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 19.08 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Cibiyar ta fitar da rahoton ne a yayin bikin baje kolin wallafe-wallafe na dijital na kasa da kasa na kasar Sin karo na 14, da aka fara a ranar Asabar a birnin Haikou, babban birnin lardin Hainan na kudancin kasar Sin.
Rahoton ya ce, ya zuwa karshen shekarar 2023, yawan masu karanta adabi ta yanar gizo a kasar Sin ya kai miliyan 537. Kana, matsakaicin darajar kasuwar littattafan yanar gizo na kasar Sin a ketare ya zarce yuan biliyan 4, wanda ya shafi kasashe da yankuna sama da 200.
Shugaban cibiyar ta CAPP Wei Yushan ya ce, al'adun gargajiya sun zama muhimmin jigo a cikin nau'ikan littattafan al'adu na intanet na kasar Sin, ciki har da littattafan adabi, cartoon da wasanni. (Yahaya)