Jirgin ruwa mai aikin jiyya na Sin ya kammala aiki a Kongon Brazzaville ya tafi Gabon
2024-09-23 14:25:14 CGTN Hausa
Jirgin ruwan soja mai aikin jinya na kasar Sin da ake kira “Ark Peace” dake gudanar da aikin ba da jinya mai taken “Mission Harmony-2024” ya kammala aikinsa a Kongon Brazzaville, ya bar tashar jirgin ruwa ta Pointe Noire, a jiya Lahadi da misali karfe 10 da safe.
A cikin wa’adin aikinsa na kwanaki 7, jirgin ya karbi marasa lafiya 4450, da gudanar da aikin binciken lafiya sau 2300, da yin tiyata 127. Ban da karbar marasa lafiya, jirgin ya tura rukunonin masana zuwa asibitoci daban-daban a kasar, inda aka zurfafa mu’ammala da cudanya da kara amincewa da juna.
Firaministan kasar Kongon Brazzaville Anatolc Collinet Makosso ya bayyana cewa, ziyarar jirgin a wannan karo muhimmin aikin jin kai ne da ake gudanarwa, lamarin da ya bayyana zumuncin kasashen biyu a cikin shekaru 60 da suka gabata, kuma ya gaggauta samun ci gaba na bangarorin biyu cikin hadin gwiwa karkashin tsarin shawarar “ziri daya da hanya daya”. (Amina Xu)