Kafa karamin rukuni domin mayar da wani sashe saniyar ware ba zai haifar da da mai ido ba
2024-09-23 19:54:13 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce kafa wani karamin rukuni domin mayar da wani sashe saniyar ware, ba zai haifar da da mai ido ba, kuma hakan zai gurgunta yanayin amincewa juna, da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan a yau Litinin yayin da yake jagorantar taron manema labarai, lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi game da tsokacin da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi, game da tsarin dandalin hadakar kasashe hudu, wato Amurka, da Japan, da India da Australia, ya ce wannan hadaka ba komai ba ce illa wani makami da Amurka ke son amfani da shi wajen dakile kasar Sin, da kuma tabbatar da babakerenta.
Jami’in ya ce har kullum Sin na yayata cewa, bai dace hadin gwiwa tsakanin kasashe ya zama makamin mayar da wani bangare saniyar ware ba, bare kuma illata moriyar wani bangare.
Game da amincewa da aka yi da yarjejeniyar cin gajiya daga fasahohin dijital na duniya bisa tsari, yayin taron kolin MDD kan makomar duniya, Lin Jian ya ce Sin na maraba da hakan. Kuma a mataki na gaba, Sin za ta yi aiki tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen ingiza matakan aiwatar da yarjejeniyar, tare da hada hannu wajen gina al’ummar duniya ta dijital mai makomar bai daya. (Saminu Alhassan)