logo

HAUSA

Za a gudanar da taron tattaunawa tsakanin magadan biranen kasa da kasa

2024-09-23 11:31:52 CGTN Hausa

 

Za a gudanar da taron tattaunawa tsakanin magadan biranen kasa da kasa, kana dandalin magadan biranen kasa da kasa karo na 9 a ran 25 ga watan nan da muke ciki a birnin Hangzhou. Magada ko wakilansu daga biranen kasa da kasa 24 na kasashe ko yankuna 15, da kuma wakilan jakadun kasa da kasa dake kasar Sin za su taru a birnin Hangzhou don yin mu’ammala da tuntubar juna bisa tunani na bude kofa da hangen nesa kan sabon tunanin gudanar da harkokin birane, da ma habaka samun bunkasuwa mai dorewa.

Hangzhou na mallakar wuraren al’adun gargajiya mafi shahara na duniya guda 3, wato tabkin Xihu da sashin Hangzhou na kogin jigilar hajojin da aka haka a lokacin da, da abubuwan tarihi da suka rage na tsohon garin Liangzhu, wanda ya kulla abota da birane masu sada zumunta 31 a duniya da kafa huldar sada zumunta da biranen ketare 42, bisa tushensa mai inganci na al’adu da saurin bunkasuwar tattalin arzikin yanar gizo da yanayin kasuwanci mai kyau da ci gaba mai armashi. A matsayin birnin dake karbar bakuncin wannan taro, Hangzhou zai taka rawar zurfafa mu’ammalar birane daban-daban da ingiza bude kofa da hadin gwiwarsu. (Amina Xu)