logo

HAUSA

Bamako: kasuwanni 7 na dabobbi aka rufe bisa dalilai na tsaro

2024-09-22 19:42:00 CMG Hausa

A kasar Mali, hukumonin kasar ne suka dauki matakin rufe wasu kasuwannin bisashe guda bakwai, inda aka rufe su ne bisa dalilin matsalolin tsaro. Matakin da aka dauka a ranar jiya Asabar, kwanaki hudu bayan harin 'yan ta''adda a birnin Bamako.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Gwamnan birnin Bamako ya dauki wannan muhimmin mataki da aka dauka a ranar alhamis 19 ga wata, na rufe wasu kasuwannin saida dabobbi da ke birnin Bamako da kewaye. Matakin da ya biwo kwanaki hudu, bayan harin da aka kai a makarantar jami'an tsaron jandarma ta Faladie.

A jimilce kasuwanni 7 matakin ya shafa, su ne kasuwar bisashe ta Lafiabougou, kasuwar bisashe ta Faladie Solola da kasuwar bisashe ta Zone Aéroportuaire, da kasuwar bisashe ta Niamane, da kasuwar bisashe ta Djelibougou da kuma kasuwar bisashe ta Zone Industrielle.

A cewar gwamna Abdoulaye Coulibaly, an dauki wannan mataki bisa dalili na tsaro. Sai dai duk da haka rufe wadannan kasuwanni kwanaki hudu bayan harin Faladie ya nuna damuwar mazauna birnin Bamako da kewaye.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.