logo

HAUSA

Xi ya mika gaisuwa ga manoma gabannin bikin girbi na manoma

2024-09-21 19:55:08 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya mika gaisuwar ban girma a madadin kwamitin kolin JKS ga manoma da ma’aikatan aikin gona a karkara gabannin bikin girbin manoma karo na bakwai.

Xi, wanda shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya jaddada cewa, dole ne a yi duk mai yiwuwa wajen inganta tattalin arzikin aikin gona, da kara yawan kudin shigar manoma, da samar da karin kuzari cikin karkara, da samar da fa'ida ta zahiri ga manoma. (Yahaya)