Chadi ta karyata zancen dawowar sojojin Amurka a cewar wata sanarwa ta rundunar sojojin Amurka
2024-09-21 21:13:17 CMG Hausa
Watanni 6 bayan ficewa sojojin Amurka da ke kasar Chadi bisa bukatar hukumomin wannan kasa da ke yankin Sahel, rundunar sojojin Amurka ta sanar cewa za ta sake maido da sojojinta ba da jimawa ba, sai dai wannan sanarwa ba ta gamsar da hukumomin Chadi ba.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Ita dai wannan sanarwa ta fito ta bakin Janar Kenneth Ekman, na hedkwatar rundunar sojojin Amurka reshen Afrika AFRICOM a cikin wata hira tare da VOA da aka ruwaito a ranar jiya 20 ga watan Satumban shekarar 2024.
Gwamnatin Chadi ba ta jira ba domin karyata wannan labari kwata kwata.
A cikin wannan hira ne, Janar Kenneth Ekman ya tabbatar cewa sojojin Amurka za su dawo Chadi, bisa bukatar hukumomin N’Djamena, in ji babban sojan Amurka.
Sai dai shugaban diplomasiyyar Chadi Abderamane Koulamallah ya yi watsi da wannan batu, tare da jaddada cewa ba mu da wata alaka tare da sojojin Amurka, mun karyata wannan zance, ba mu yi tattaunawa ba tare da gwamnatin Amurka kan dawowarsu a kasar Chadi.
Haka kuma, gwamnatin Chadi ta sanar a cikin wata sanarwa ta ranar jiya 20 ga wata cewa, yana da muhimmanci na tunatar cewa Chadi, kasa ce mai cikakken ‘yanci, kuma game da batun tsaron kasarta tare da wasu kasashen duniya, ita kadai take da wannan hurumi.
Idan ba ku manta ba, kasar Chadi ta bukaci kasar Amurka da ta janye sojojinta kafin zaben shugaban kasar na cikin watan Mayun shekarar 2024.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.