Najeriya ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfain kasar Rasha domin farfado da kamfanin mulmula karafa na Ajakuta
2024-09-21 16:40:22 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin kasar Rasha TPE domin farfado da kamfanin mulmula karafa na Ajakuta tare kuma da karasa aikin ginin kamfanin hakar ma’adanin karfe NIOMCO duka da suke a jihar Kogi dake arewa ta tsakiyar Najeriya.
Ministan bunkasa harkokin samar da karafa na Najeriya Alhaji Shu’aibu Abubakar Audu shi ne ya sanya hannun a madadin gwamnatin Najeriya lokacin da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa birnin Moscow domin ziyarar aiki daga ranar 14 zuwa 21 ga wannan wata na Satumba.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kamar dai yadda yake kunshe cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun babbar jami’ar hulda da jama’a na ma’aikatar, Salamatu F. Jibaniya wadda kuma aka rabawa manema labaru jiya juma’a 20 ga wata a birnin Abuja, ta yi bayanin cewa sanya hannu kan yarjejeniyar ya biyo bayan ziyarar da shugabannin kamfanin suka kawo nan Najeriya a watan Agustan wannan shekara, inda suka duba kamfanonin guda biyu, wanda hakan ya sanya gwamnatin kasar ta Rasha gayyatar wakilan na Najeriya zuwa birnin na Moscow.
Sanarwar ta ambato ministan na cewa, sanya hannun kan wannan yarjejeniya wani babban mataki ne da aka kai ga takawa wajen samar da yanayi mai dorewa na cigaban harkokin masana’antu a tsarin tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce farfado da bangaren samar da karafan zai taimaka wajen rage yawan dogaro da Najeriya ke yi wajen shigo da karafa daga kasashen ketare wanda take kashe sama da dala biliyan 4 a duk shekara.
Mataimakin ministan ciniki da masana’antu na kasar Rasha Mr. Alecey V. Gruzdev shi ne ya jagoranci sanya hannu kan wannan yarjejeniya tare da shugabannin kamfanin na TPE.
Dukkannin bangarorin biyu sun sha alwashin tabbatar da yin cikakken aiki da abubuwa da suke kunshe cikin wannan yarjejeniya na farfado da kamfanonin biyu wanda aka yi hasashen cewa, za su samar da guraben aiki na kai tsaye ga ‘yan Najeriya sama da dubu dari biyar, sannan zai karfafa tattalin arzikin kasar wajen samar da biliyoyin daloli, wanda hakan zai taimaka mutuka wajen cimma burin shugaba Bola Tinubu na bunkasa tattalin arzikin kasar zuwa dala tiriliyon 1 nan da shekara ta 2030. (Garba Abdullahi Bagwai)