logo

HAUSA

Beijing ya karbi bakuncin taro kan gado da musayar al’adu

2024-09-20 14:12:03 CMG Hausa

An bude dandalin taron al’adu na Beijing na 2024, jiya Alhamis a birnin Beijing, wanda ya samu mahalarta sama da 800 daga ciki da wajen kasar Sin, dake tattaunawa kan maudu’in da ya danganci gadon al’adu da raya su da ma musaya.

Yayin taron, mahalarta sun bayyana muhimmancin bukatar dake akwai ta inganta musaya tsakanin mabanbanta al’ummu, da aiwatar da shawarar inganta zaman takewa tsakanin mabanbanta al’ummu, da inganta musaya da hadin gwiwa tsakanin jama’ar kasa da kasa domin kara fahimtar juna da kulla abota a tsakaninsu.

A cewar mashirya taron, baya ga haka, bikin bude dandalin da babban taronsa da zai dauki tsawon yini 3, zai karbi bakuncin wasu taruka 6 da kuma shirye-shiryen al’adu da za a gabatar ga kwararru da sauran jama’a. (Fa’iza Mustapha)