logo

HAUSA

Firaministan Sin ya taya murnar bude taron hukumar IAEA karo na 68

2024-09-18 10:30:01 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya aike da sakon taya murna ga babban taro karo na 68 na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA).

Cikin sakon da ya aike a ranar Litinin, Li Qiang ya bayyana cewa, makamashin nukiliya na da muhimmanci wajen samar da makamashi mai tsafta, yana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da tsarin tsaron nukiliya a duniya, wanda ya mayar da hankali kan tabbatar da adalci da hadin gwiwar moriyar juna.

Ya ce tun bayan shigar Sin cikin hukumar IAEA shekaru 40 da suka gabata, ta kasance mai goyon bayan ayyukan hukumar da ingantattun matakai, yana mai cewa, bangarorin biyu sun hada gwiwa a dukkan fannonin rayawa da amfani da makamashin nukiliya, da tabbatar da tsaro da amincin makamashin, da hana yaduwarsa, kuma an samu kyawawan sakamako tare da bayar da gagarumar gudunmuwa ga ayyukan rayawa da tafiyar da harkokin da suka shafi makamashin nukuliya a duniya.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta shirya kara karfafa hadin gwiwa da hukumar IAEA da sauran kasashe mambobi wajen kara tafiyar da harkokin da suka shafi makamashin cikin adalci da sanin ya kamata da samar da ci gaban harkokin makamashin ta kowacce fuska da hadin gwiwa bisa gaskiya da tsari. (Fa’iza Msutapha)