Hadarin mota ya hallaka mutane 40 a Kaduna ta Najeriya
2024-09-18 10:46:19 CMG Hausa
A kalla mutane 40 ne suka rasu, sakamakon wani hadarin mota da ya rutsa da su a garin Saminaka na jihar Kaduna ta arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotanni sun ce, wata mota kirar bas da wata babbar motar dakon kaya ne suka yi karo, wanda hakan ya haifar da rasuwar fasinjoji da dama.
Wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ta ce baya ga wadanda hadarin ya hallaka, karin wasu mutanen sun ji raunuka, sakamakon hadarin da ya rutsa da masu bikin Maulidi a ranar Lahadi.
Sanarwar da mista Onanuga ya fitar a madadin shugaba Bola Tinubu, ta ce shugaban Najeriyar na mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, da gwamnatocin jihohin Kaduna da Plateau, da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Kaza lika cikin sanarwar, shugaba Tinubu ya umarci hukumar kare hadurra ta kasar FRSC, da ta inganta matakan sanya ido, da rage adadin hadurran dake aukuwa a kan titunan kasar baki daya. (Saminu Alhassan)