Kasar Sin za ta sanya takunkumi kan kamfanonin sojan Amurka wadanda suka sayar da makamai ga yankin Taiwan
2024-09-18 21:04:42 CMG Hausa
Kasar Sin ta yanke shawarar kakaba takunkumi kan wasu kamfanonin sojan Amurka guda 9 kan sayar da makamai ga yankin Taiwan, a cewar matakin da kasar ta dauka wanda aka wallafa a shafin intanet na ma'aikatar harkokin wajen kasar a yau Laraba.
Matakin ya yi nuni da cewa, a baya-bayan nan Amurka ta sake sanar da shirin sayar da makamai ga yankin Taiwan, wanda ya sabawa manufar “Sin daya tak a duniya” da kuma sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, da kuma kawo cikas ga 'yancin kan kasar Sin da kuma cikakkun yankunanta.
Bisa la'akari da batutuwa na 3, 4, 6, 9 da 15 na dokar yaki da takunkumin da kasashen ketare suka kababawa kasar Sin, Sin ta yanke shawarar daukar matakai kan kamfanin Sierra Nevada Corporation, Stick Rudder Enterprises LLC, Cubic Corporation, S3 AeroDefense, TCOM Limited Partnership, TextOre, Planate Management Group, ACT1 Federal da Exovera, ta hanyar kwace kadarorinsu duka dake kasar Sin. Kana, an haramtawa kungiyoyi da daidaikun mutane a kasar Sin yin mu'amala, hadin gwiwa da sauran ayyuka tare da kamfanonin da aka ambata. Matakin ya fara aiki daga ranar 18 ga watan Satumban shekarar 2024. (Yahaya)