logo

HAUSA

Hukumar Najeriya: ya kamata al’ummar kasar su kara kasancewa cikin shirin kare kai daga fuskantar ambaliyar ruwa

2024-09-18 10:13:19 CMG Hausa

Hukumar lura da madatsun ruwa a tarayyar Najeriya ta ja hankalin al’ummar kasar cewa su zama cikin shirin kare kai daga fuskantar ambaliyar ruwa a nan gaba, kasancewar kasar Kamaru ta fara rage ruwan dake Dam din Lagdo.

Daraktan-janaral na hukumar Alhaji Umaru Mohammed ne ya sanar da hakan da yammacin jiya Talata 17 ga wata a birnin Abuja cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai. Ya ce, duk da dai za a rinka sakin ruwan sannu a hankali ne amma akwai bukatar gwamnati da al’umma su kwana cikin shiri.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Alhaji Umaru Muhammed ya ce, mahukuntan kasar ta Kamaru sun tabbatar da cewa, za su dauki mako guda suna sakin ruwan har zuwa lokacin da aka ga cewa mizanin ruwan dake Dam din ya daidaita.

Shugaban hukumar lura da harkokin madatsun ruwan na Najeriya ya ci gaba da bayanin cewa, kamar dai yadda aka tsara a duk sakan guda za a saki Cubic Mita dari, wanda ya kama adadin cubic mita miliyan 8.64 a rana guda, kuma tun daga jiya Talata 17 ga wata aka fara sakin ruwan.

Ya ce akwai yiwuwar kara adadin ruwan da za a rinka fitarwa a duk sakan daya zuwa cubic mita dubu daya.

Darakta-janaral din ya kara da cewa, za a yi kokarin ganin ruwan da za a fitar ba zai fi karfin ruwan dake kogin Benue ba kasancewar ta wajen zai gangarowa duk dai don tabbatar da kare wasu yankuna na Najeriya daga fuskantar ambaliyar ruwa.

Amma da duk da haka, shugaban hukumar lura da madatsun ruwan ta Najeriya ya bukaci gwamnatin tarayya da kananan hukumomi da jihohi musamman wadanda dake da iyaka da kogin Benue din kamar Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa, Kogi, Edo, Delta, Anambra, Bayelsa, Cross River da kuma Rivers da su kara kasancewa cikin shiri sosai bisa tunanin ko adadin ruwan da za a rinka fitarwa daga madatsar ruwan ta Kamaru ya yi yawan da zai iya yin barna, yayin da hukumar za ta ci gaba da sanya ido tare da fadakar da al’umma a kai a kai. (Garba Abdullahi Bagwai)