Mali: An ji karar bindigogi da fashewar boma bomai a birnin Bamako
2024-09-17 20:25:32 CMG Hausa
A kasar Mali, a yau da sassafen ranar Talata 17 ga watan Satumban shekarar 2024, mazauna Bamako, babban birnin kasar suka tashi cikin karar bindigogi da fashewar boma bomai, bayan da wasu mutane dauke da makamai suka kai hari kan sansanin jami’an tsaro na jandarma.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Majiyoyi da dama ne suka bayyana jin karar bindigogi a Bamako, babban birnin kasar Mali, harbe harben da aka fara wajajen karfe biyar na safen ranar yau Talata 17 ga watan Satumban shekarar 2024, bisa agogon wurin.
Karar bindigogi da kuma fashewar boma bomai mazauna birnin bamako suka wayi gari da su, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP na kasar Faransa.
Mutane dauke da makamai da ba’a tantance su ba, sun kai hari a yau da safe a kan sansanin jami’an tsaro na jandarma da ke birnin Bamako, a cewar wani babban jami’in ofishin jandarma da ya bukaci a sakaya sunansa.
Harbe harben sun guduna a kewayen sansanin jami’an tsaro na jandarma da ke cikin unguwar Faladje, a kudancin birnin Bamako kuma arewa da filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Modibo Keita.
A cewar majiyar da ke wurin, an rufe hanyoyi a bangaren da harin ya faru.
Saidai a cewar rundunar sojojin kasar Mali na FAMA, an kawo karshen harin, tare da kama mahara biyu 2, a cewar majiyar sojojin FAMA.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.