logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen gamayyar kasashen yankin Sahel na AES sun yi wani zaman taro a birnin Bamako

2024-09-17 16:31:13 CMG Hausa

A ranar jiya Litinin 16 ga watan Satumban shekarar 2024, aka bude ayyukan taron farko na ministocin harkokin wajen gamayyar kasashen yankin Sahel AES a birnin Bamako, a karkashin jagorancin Abdoulaye Diop, ministan harkokin wajen kasar Mali.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Wannan muhimmiyar haduwar ministocin ta zo daidai da cikon shekara guda da sanya hannu kan yarjejeniyar Liptako-Gourma da ke tabbatar da hadakar kasashen yankin Sahel na AES, da ta samu halartar ministan harkokin wajen Burkina Faso Karamako Jean Marie Traore da kuma Bakary Yaou Sangare, ministan harkokin wajen kasar Nijar.

A yayin bikin bude taron, ministocin harkokin wajen kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali sun jinjinawa tsinkaye da jagoranci na gari na shugabannin kasashensu da suka sanya a gabansu wani hangen makoma mai haske ta hadin gwiwa domin moriyar al’ummomin kasashensu.

Kafa gamayyar kasashen yankin Sahel, a ranar 6 ga watan Yulin shekarar 2024 a birnin Yamai, na kasancewa a wannan mataki, wata niyya mai fa’ida ta kishin Afrika na manyan hukumomin kasashen uku domin cimma muradun dunkulewar tattalin arziki da na al’umma da ci gaba mai armashi na moriyar juna a cikin shiyyar AES.

Daga bisani ministocin harkokin wajen kasashen uku sun yi amfani da wannan dama domin yin allawadai da kasashen yammacin duniya da ke hada kai da ‘yan ta’adda domin kawo tashin hankali cikin kasashen yankin Sahel.

Haka kuma wannan zaman taro na ministocin harkokin wajen kasashen Yankin Sahel zai duba da amincewa da manufofin siyasa da na tattalin arziki bisa niyyar kasashen na kama akibla guda daga dukkan fannoni.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.