Kafar CMG ta zanta da shugaban gwamnatin Norway
2024-09-14 15:23:02 CGTN Hausa
A kwanakin baya, shugaban gwamnatin Norway, Jonas Gahr Store ya kawo ziyara Sin, karon na farko tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban gwamnatin kasar.
Jonas Gahr Store wanda ya zanta da wakilin CMG yayin da yake bulaguro cikin jirgin kasa mai saurin tafiya, ya ce tafiya Shanghai daga Beijing ta hanyar jirgin kasa mai saurin tafiya abu ne mai ban sha’awa, inda ya ce ana iya aiki da karatu da barci da more rayuwa a cikin jirgin. Saurin jirgin ya burge shi matuka, abin da ya ba shi damar gano muhimmin bangaren ci gaban kasar Sin. Ya ce ya kuma fahimci cewa, Sin na yin la’akari da gaggauta raya layukan dogo, yana mai bayyana hakan a matsayin wani abu na wayewar kai kasancewar yadda ake shimfida layukan dogo a wuraren dake da dimbin mutane. (Amina Xu)