Xi ya bukaci a yi kokarin tafiyar da majalisar wakilan jama’ar kasar yadda ya kamata
2024-09-14 20:39:28 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar ci gaba da daukakawa da inganta tsarin tafiyar da majalisar wakilan jama’ar kasar, wanda shi ne kashin bayan tsarin siyasar kasar, yadda ya kamata. Shugaban ya bayyana haka ne yayin wani taro a yau Asabar, domin murnar cikar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin shekaru 70 da kafuwa.
Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban kwamitin koli na sojin kasar, ya nanata bukatar kara kwarin gwiwa kan hanya da tunani da tsari da al’adun gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)