logo

HAUSA

Taron tsaro na Xiangshan ya samar da wani dandali da kasashe masu tasowa za su shawo kan matsalolin tsaro

2024-09-14 16:28:52 CMG Hausa

Taron tsaro na Xiangshan na Beijing karo na 11 da aka kaddamar ranar Alhamis, ya kara sautin muryar kasashe masu tasowa kan batutuwan tsaro, inda sama da kaso 60 na mahalarta suka fito daga kasashe masu tasowa.

Bisa wani rahoton da aka fitar a hukumance, a karon farko, an sanya kasashe masu tasowa cikin ajandar taron, haka kuma a karon farko, an gayyaci malamai da dama daga nahiyoyin Asiya da Afrika, har da kasar Sin, domin su tattauna kan batutuwan masu ruwa da tsaki.

Jia Qingguo, farfesa a Tsangayar Nazarin Harkokin Kasashen Waje ta Jami’ar Peking, ta bayyana yayin wani taron tattaunawa cewa, yayin da karfin kasashe masu tasowa ke karuwa, abu ne mai muhimmanci a shawo kan damuwarsu, lamarin da ta ce, zai bayar da gudunmuwa ga samar da daidaito ga yanayin tsarin duniya.

Shi kuwa Joseph Kahama, babban sakatare na kungiyar raya abota tsakanin Sin da Tanzania, yabawa kasar Sin ya yi bisa jagorantar habaka hadin kan kasashe masu tasowa da yadda take kaucewa nuna bangaranci a rikice-rikicen dake wakana a shiyyoyin duniya da kuma kokarinta na shiga tsakani. Ya ce a kullum, Sin kan kasance gaba-gaba wajen daukaka dangantakarta da kasashen Afrika, haka kuma ta kulla alaka mai karfi tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)