Sin ta kulla yarjejeniyar tsarin kafa huldar abota ta raya tattalin arziki cikin hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka 22
2024-09-13 14:06:02 CGTN Hausa
Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta ce, tana kokarin gaggauta kulla yarjejeniyar tsarin kafa huldar abota ta raya tattalin arziki cikin hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka 22.
Yayin taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka da aka gudanar a nan birnin Beijing, Sin ta kulla yarjejeniyar da kasashen Afirka 22 ciki hadda Habasha, Equatorial Guinea da Kongo Brazzaville da Kongo Kinshasa da Gabon da Djibouti da kuma Zimbabwe da Guinea-Bissau da Comoros da Cote d'Ivoire. Kana da Liberia da Libya da Madagascar da Mauritania, har da Sudan ta kudu da Saliyo da Seychelles da Sao Tome da Principe da Uganda da Chad da Africa ta tsakiya da sauransu.
Wannan yarjejeniya ta aza tubali ga shawarwarin da za a yi game da ciniki da zuba jari da sauransu a nan gaba, da kuma ba da tabbaci mai dorewa a bangaren tsarin hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya a cikin dogon lokaci. Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da kara tuntubar kasashen Afirka dake da burin shiga wannan yarjejeniyar, da ma tabbatar da ci gaban da aka samu a taron kolin da kuma habaka bude kofa da dogaro da kai, da ma kokarin amfanawa al’umommin bangarorin biyu nan gaba. (Amina Xu)