Xi ya yi kira da a zurfafa gyare-gyare a Gansu domin daukaka zamanatarwa irin ta Sin
2024-09-13 20:35:36 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar, ya zurfafa gyare-gyare, da kirkire-kirkire da aiwatar da kwararan ayyuka domin inganta walwalar jama’a da ci gaban yankin, tare da rubuta wani babi na Gansu a aikin zamanantar da kasar Sin.
Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin rangadin da ya yi daga ranar Talata zuwa yau Juma’a.
Ya ce kamata ya yi lardin Gansu, ya dauki kwararan matakai na inganta karewa da farfado da muhallin halittu da gaggauta yin gyare-gyare wajen amfani da makamashi mai tsafta da rage fitar da hayakin Carbon da kara zurfafa gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, da inganta farfado da yankunan karkara ta kowacce fuska da kyautata walwalar jama’a da kuma karfafa hadin kai tsakanin mabambantan kabilu. (Fa’iza Mustapha)