Sin ta bukaci Birtaniya ta girmama gaskiya ta kuma daina nuna yatsa
2024-09-13 21:37:45 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bukaci Birtaniya ta girmama gaskiya da hujjar cewa yankin Hong Kong ya dawo karkashin ikon babban yankin kasar Sin tsawon shekaru 27 da suka gabata, kuma ta daina tsoma baki ko yanke hukunci kan batutuwan yankin.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka, lokacin da take tsokaci dangane da wani rahoto da a baya bayan nan gwamnatin Birtaniya ta fitar, wanda ta kira “rahoton rabin shekara don gane da batun Hong Kong.” Mao Ning ta kara da cewa, batutuwan Hong Kong, batutuwa ne na cikin gida da suka shafi kasar Sin kadai. (Fa’iza Mustapha)