logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Lanzhou na Sin

2024-09-12 13:51:41 CMG Hausa

Da yammacin jiya Laraba ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya kammala rangadi cikin nasara a sassan unguwar Zaolin ta yamma dake gundumar Anning, da yankin gadar Zhongshan, duk a cikin birnin Lanzhou na lardin Gansu, dake yammacin kasar Sin.

Yayin rangadin, shugaba Xi ya nazarci ayyukan samar da saukin rayuwa, da na hidimomi da aka samarwa al’ummun wuraren, tare da na karfafa jagorancin kula da jin dadin jama’a, da ingiza kare muhallin halittu a yankunan rawayar kogi.  (Saminu Alhasan)