Li Qiang ya fara ziyarar aikinsa a UAE
2024-09-12 12:42:35 CGTN Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Abu Dhabi, hedkwatar hadaddiyar daular Larabawa a daren jiya Laraba, bisa gayyatar da mataimakin shugaba, kana firaministan kasar Mansour bin Zayed Al Nahya ya yi masa.
Li Qiang yana sa ran zurfafa mu’ammala da shugabannin kasar, da abokai daga bangarori daban-daban na kasar, da ma gaggauta zurfafa dangantakar kasashen biyu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare, ta amfani da zarafi mai kyau na cika shekaru 40 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu bisa jagorancin shugabanninsu.
Li Qiang ya isa Abu Dhabi ne bayan ya kammala jagorancin taron kwamitin hadin kai na manyan jami’an Sin da Saudiyya karo na 4, da kammala ziyarar aikinsa a Saudiyya. (Amina Xu)