Yawan kudin shiga da manyan kamfanoni 500 na kasar Sin suka samu a shekarar 2024 ya kai Yuan triliyan 110
2024-09-11 14:45:10 CMG Hausa
A yau ne, kungiyar hadin gwiwar kamfanonin Sin da kungiyar ‘yan kasuwa ta kasar Sin suka fitar da jerin sunayen manyan kamfanoni 500 na kasar Sin na shekarar 2024. Game da ribar da kamfanoni suka samu, an ce, yawan ribar da manyan kamfanoni 500 na kasar Sin suka samu a shekarar 2024 ya kai Yuan triliyan 4.51, wanda ya karu da kashi 5.01 cikin dari, bisa na shekarar bara. Kana yawan kudin shiga da kamfanonin suka samu ya kai Yuan triliyan 110 a karo na farko a tarihi, wanda ya karu da kashi 1.58 cikin dari, bisa jimillar bara.
Ban da wannan kuma, fiye da rabin kamfanonin sun zuba karin jari ga bangaren kirkire-kirkire, inda kamfanoni 5 a cikin kamfanonin 10 mafi yin kirkire-kirkire su ne kamfanoni masu samar da na’urorin sadarwa. (Zainab Zhang)