logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da tsoma baki da Amurka ta yi cikin harkokin Hong Kong

2024-09-11 20:31:10 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana rashin gamsuwa tare da adawa da yunkurin Amurka na amfani da batutuwan Hong Kong wajen danne ci gaban yankin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana yayin taron manema labarai na yau Laraba cewa, majalisar wakilan Amurka na duba yuwuwar zartar da dokar soke gatanci da kariyar da ofishin kula da harkokin cinikayya da tattalin arziki na Hong Kong (HKETO) ke da su.

A cewar Mao Ning, gwamnatin yankin musammam na Hong Kong ce ta kafa ofishin mai kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya a ketare, kuma nasarar da ya samu da yadda harkokinsa ke gudana, sun dace da fadada hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Hong Kong da sauran kasashe da yankuna, domin samun sakamako na moriyar juna.

Ta kara da cewa, kudurin dokar ya siyasantar da yanayin hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki da aka saba yi, tare da neman cimma wata manufa. Haka kuma ya keta sahihancin hukumomin Hong Kong dake ketare, tana cewa, abu ne da bai dace ba. (Fa’iza Mustapha)