Kasar Sin za ta zurfafa hadin gwiwa da sauran kasashe a bangaren tsaron intanet
2024-09-11 19:26:38 CMG Hausa
Tsarin shirye shiryen da aka amince da su yayin taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, wanda aka kammala a baya baya nan, ya tanadi cewa, Sin da Afrika za su karfafa hadin gwiwa a bangarorin tsaron intanet.
Don gane da haka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta bayyana yayin taron manema labarai na yau Laraba cewa, bisa tsarin, Sin da Afrika za su karfafa musayar bayanai tsakaninsu, da biyayya da amfani da sabbin fasahohi da dokoki da ka’idojin intanet, da hada hannu wajen tsara ka’idojin jagorantar harkokin da suka shafi intanet.
Mao Ning ta kara da cewa, yayin da wannan makon ya kasance makon wayar da kai game da tsaron intanet a kasar Sin, Sin za ta ci gaba da hada hannu da dukkan bangarori wajen kare tsaron intanet ta yadda mutane za su kara amfana da shi. (Fa’iza Mustapha)