logo

HAUSA

Kasashen Sin da Rasha sun amince su karfafa shawarwari da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare

2024-09-11 10:04:39 CMG Hausa

Darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a yayin ganawarsa da sakataren kwamitin tsaro na kasar Rasha Sergei Shoigu a jiya Talata a birnin St. Petersburg cewa, kasar Sin a shirye take ta karfafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Rasha, da kuma ci gaba da inganta shawarwari bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. 

A yayin taron, Wang ya kara da cewa, duk da ana fuskantar sauye-sauye da ba a taba irinsu ba a cikin karni, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha na cikin kwanciyar hankali da daidaito wanda ke da nasaba da jagorancin shugabannin kasashen biyu.

A nasa bangare kuwa, Shoigu ya bayyana cewa, yin mu'amala mai inganci tsakanin Rasha da Sin da hadin gwiwa mai kaykkyawar sakamako a fannoni daban-daban, sun nuna girman matsayin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Rasha da Sin. (Mohammed Yahaya)