CMG ya sa hannu kan sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwar watsa gasar La Liga
2024-09-11 14:05:28 CMG Hausa
Yayin da firaministan kasar Spaniya Pedro Sanchez yake ziyara a kasar Sin, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG da kungiyar kawancen wasan kwallon kafa ta Spaniya sun sanar a jiya ranar 10 ga wannan wata cewa, sun cimma daidaito kan hadin gwiwarsu a fannin watsa gasar La Liga ta wani sabon wa’adi, don haka CMG zai watsa gasar La Liga a wannan kakar wasa cikin shirye-shiryen telabijin dinsa. (Zainab Zhang)